Za A Fara Sayar da Shinkafa ‘Yar Nijeriya A Farashi Naira Dubu Shida

shinkafa

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa Na Nijeriya, (RIFAN) ya bayyana cewar shirye-shirye sun yi nisa domin ganin an rage farashin shinkafar da ake sarrafawa Nijeriya daga naira dubu 18 zuwa dubu 6, nan da wasu ‘yan watannin masu zuwa.

Shugaban kungiyar, Alhaji Aminu Goronyo ne ya fadi haka a lokacin wata ganawa da Kungiyar Masu Sarrafa Shinkafa da kuma Ministan Gona, Cif Audu Ogbe, inda suka cimma matsaya cewar, za a rage kudin shinkafar, duk da cewa sun yi kokarin ganin farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya tsaya a naira dubu 13, amma yanzu ana sa ran nan da ‘yan wasu watanni farashin zai dawo naira dubu 6 kacal. (Leadership hausa)

Comments

comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *