Hukumar Ciyar Da Ɗalibai Ta Ja Kunnen Jami’anta A Zamfara

Free-school-feeding-Programme

Hukumar Ciyar da Ɗaliban Jihar Zamfara Ƙarƙashin Jagorancin Babban Sakataren Hukumar, Sa’in Zamfara, Malam Atiku Sani Maradun ta ja kunnen jami’an hukumar masu kula da ciyar da Ɗalibai a makarantun Sakandire da su ji tsoran Allah wajen ba ɗalibai abincin da aka basu, kuma duk wanda ta ka kama da maguɗi wajen ciyarwar zai gamu da hukunci. Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da ake rabon kayayyakin a ofishin hukumar .

Malam Atiku ya bayyana cewa, gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdul’aziz Yari ta na iyaka ƙoƙarinta wajen ciyar da ɗaliban Jihar da kuma jin daɗi da walwalar su. “Fatan mu shi ne bamu son jnkiri wajen dawowan ɗalibai, don akwai abinci isasshe da kuma wasu abubuwan da zasu taimawa ɗaliban ko da iyayensa basu kawo masa komai ba,Wanda muke badawa ya isa. Don haka na ke kira da duk iyaye da suture ‘ya’yansu makaranta, gwamnati ta tanadi abubuwan buƙatar su.

“Kuma lokaci bayan lokaci wannan hukumar, za mu ci gaba da zagayawa don ganin yadda ake ba ɗalibai abinci. Idan muka samu saɓani daga tsarin da muka bada, lallai zamu hukunta mutum.” inji shi.

Malam Atiku ya kuma ba jami’an ciyarwar shawara da su riƙa sanar da shugabannin makarantu halin da suke ciki, don samun shawara da kuma kauce wa matsala. Domin fatan wannnan Hukumar shi ne Samar wa da ɗalibai ingantaccen abinci, don samun ingantacen ilimi. ( (Leadership hausa)

Comments

comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *