HAUSA VERSION: Sanata Danjuma Yayi Alla-wadai da Rusa Tubalin Ginin Barikin Sojoji

Danjuma Laah

Takardar Jawabin mai Girma Sanatan Kudancin Kaduna, Sanata Danjuma Tella La’ah ga Manema labarai kan Alla-wadai da Rusa Tubalin Ginin Barikin Sojoji na Garin Bakin Kogi.

Ya ku taron ‘yan jarida. Hakika ina mai shaida muku cewa nayi matukar damuwa da shiga dimuwa da jimami game da labarin rusa harsashin ginin barikin sojojin da ake shirin ginawa a garin Bakin Kogi, Kusa da kafanchan a wani lokaci cikin makon da ya gabata.

Hakika wannan ba wani abu ne da za a dauke shi kawai a matsayin aikin assha, kuma wani abu da ba za mu taba yarda da shi ba kawai, wannan wani mummunar sako ne da wasu marasa son zaman lafiya ke aikewa da shi don dai kawai su kange ci gaban al’ummarmu da bunkasar da take hankoron kaiwa ba.

Hakika ina mai matukar bakin ciki da wannan al’amari mai ban takaici, lura da irin fadi-tashin da nayi tayi ina rokon gwamnatin tarayya da ta samar mana da alal akalla, wani matsuguni na sojoji a tsakanin garin kafanchan da kewayenta ba tun shekarara 2015.

Dole ne mu dinke barakar da ke tsakaninmu, mu kuma sabunta yarda da ‘yan uwantakar da ke tsakaninmu da kyakkyawar niyya. Lokaci yayi da zamu yi watsi da bambamce-bambamcen da ke tsakaninmu; imma na kabilanci ko na siyasa ko kuma bambamcin addini ba. Lokaci yayi da za mu manta da rarrabuwan kai, rudani da tashin hankali, domin wadannan sune turakun masifu da kuma koma baya.

Dole ne mu yi karatun ta-natsu, mu yiwa kawukanmu fada tare da dora harsashin ci gaba, don ci gaba daga inda mu ka tsaya. Mu mance da ayyukan makiyanmu, makiya son zaman lafiya da ci gaba. Mu hada hannuwanmu tare da yin aiki tukuru wajen dunkule yankinmu na kudancin Kaduna, da ma jihar Kaduna gaba daya.

Babu shakka raunin da aka yi mana akwai radadi, amma ai haka rayuwar ta gadar; idan an sha zuma yau, watarana za asha madaci, amma dai dole mu ci gaba da zama tare.

Allah cikin hikimarsa da jinkansa, ba wai ya halicce mu da yunbu mai dunkulewa ne ba kawai, ya kuma ajiye mu waje daya ne don mu yi amfani da wannan dammar wajen bunkasa kanmu daga turbayar da aka halicce mu zuwa ga mafi kyawun halitta wadanda ba ma kawai za su yi alfahari da kyawun ‘yan uwantakar da ta dunkule su waje guda kamar yunbu mai dunkulewa bane, da kuma bunkasa da ci gaba ba, har ma da bayyanar da ruhin juriya da hakuri da zaman lafiya da kuma harkar noman da aka san kudancin Kaduna da shi tuntuni ba.

Ina mai kara jaddada yin kira garemu gaba daya da mu hada kawukanmu waje daya don samun yin galaba kan wannan mummunar halin da mu ka tsinci kanmu a ciki. Mu sani cewa wadanda ke son wargaza mana yanki, muna masu tabbatar musu da babbar murya cewa, da sannu Ubangijin da mu ke bautawa zai kunyata su, maketata.

Ina mai sake yin kira ga dukkanin ‘ya’yan kudancin Kaduna masu kaunarta, daga dukkanin kabilu da addinan da mu ke da su, da su zo mu hada hannuwanmu ba tare da nuna wariya ko kabilanci ba don daukaka kudancin Kaduna.

A karshe ina mai son jaddada muku cewa, aikin da wadannan marasa son zaman lafiyar su ka aikata na rusa tubalin gina barikin sojoji da suka yi, ba da yawun mutanen kwarai na kudancin Kaduna su ka yi ba (kuma ba ma goyon bayansu), don haka na ke yin amfani da wannan dama wajen yin kira ga mahukuntar da abin ya shafa da kada su yi kasa a gwiwa wajen zakulo wadanda su ka aikata wannan aika-aika don yin maganinsu ba.

Sanata Danjuma Tella la’ah

Sanatan Kudancin Kaduna

Comments

comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *